WASHINGTON, D.C —
Hukumar NCDC da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta bada rahoton samun karin mutum 684 da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.
A sanarwar da ta fidda a daren ranar Juma’a 26 ga watan Yuni, hukumar ta ce an samu sabbin kamu mutum 259 a jihar Legas, 76 Rivers, 69 a Katsina, 66 a Delta, 46 a Rivers, 23 a Ogun.
Sauran jihohin da aka samu karin sun hada da Edo inda aka samu mutum 22, 21 a Ebonyi, 20 a birnin Tarayya Abuja, 16 a Kaduna, 10 a Ondo, 9 a Imo, 9 a Abia, 5 a Gombe, 4 a Plateau, 4 a Bauchi, 2 a Ekiti, 1 a Anambra.
Sanarwar ta kuma ce gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya yanzu ya kai 23,298, an kuma sallami mutum 8,253 daga asibiti bayan haka mutum 554 suka mutu sakamakon cutar.