A yayin da cutar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a kasashen duniya hukumar NCDC da ke kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce an samu karin mutum 603 da suka kamu da cutar a ranar Asabar 4 ga watan Yuli.
Jihar Legas inda cutar ta fi bazuwa ta samu karin mutum 135 da suka kamu da cutar.
Sauran jihohin sun hada da Edo inda aka samu karin mutum 87, 73 a birnin Tarayya Abuja, 67 a Rivers, 62 a Delta, 47 a Ogun, 20 a Kaduna, 19 a Plateau, 17 a Osun, 16 a Ondo, 15 a Enugu, 15 a Oyo, 13 a Borno, 6 a Neja, 4 a Nasarawa, 3 a Kebbi, 2 a Kano, 1 a Sokoto, 1 a Abia.
A halin yanzu, jimlar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya ta kai 28,167.
Hukumar NCDC ta kuma ce ya zuwa yanzu mutum 11,462 aka sallama daga asibiti bayan haka mutum 634 suka mutu sanadiyyar cutar.