An Samu Karancin Masu Kada Kuri'u A Jihohin Adamawa Da Taraba

An samu karancin fitowar masu zabe a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba, a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da ake yi yau Asabar, a Najeriya.

Rahotanni na cewa an samu karancin fitowar masu zabe a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba, a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da ake yi yau Asabar, a Najeriya.

Baya ga wannan kuma duk da matakan tsaron da aka ce an dauka matasa 'yan bangar siyasa sun ci karen su babu babbaka, baya ga batun masu sayen kuri'u.

Tun da sanyin safiya ne dai jama'a suka soma fita zuwa rumfunan zabe a wasu wuraren, ko da yake a wasu rumfunan zaben ba'a fito ba sosai.

Wata mai suna Laure Ahamad ta danganta lamarin na rashin fitowan da rashin cika alkawurran shugabanin dake kan mulki ke yi.

Da yake kada kuri'arsa sakataren gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha ya yaba da yadda aikin zaben ke gudana.

To sai dai kuma a nasa martanin dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar bai gamsu da yadda zaben ya gudana ba.

Ya zuwa yanzu babu wani rahoton tashin hankali a jihohin Adamawa da Taraba, yayin da aka soma hada hancin sakamakon zaben.

Saurari cikakken rahoton da Ibrahim Abdul-Aziz ya aiko mana daga Yola:

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Karancin Masu Kada Kuri'u A Jahohin Adamawa Da Taraba 03'15"