Maharban sun janye ne daga yankunan da aka kwato daga mayakan Boko Haram saboda takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu da 'yansandan jihar da ta kaiga kama wasunsu.
Sun janye ne domin nuna fushinsu da kamun da rundunar 'yansanda ta yiwa shugaban maharban tare da wasu jami'ansu.
Shugaban maharban a jihar Alhaji Muhammad Tula yace yadda suka rike amana duk membobinsu na ciki da waje su kwantar da hankulansu, su yi hakuri su koma bakin aikinsu. Yace babu abun da zai biyo baya amma hakuri yake bayarwa.
Wani kusa a kungiyar dake kula da shiyar Gombe yace tare 'yansanda suka rikesu. Yace abun da Allah ya kaddara babu mai kawar dashi. Ya godewa jama'a da masu goyon bayansu. Yace Lamidon Adamawa ya kirasu ya ja kunnuwansu. Sun fahimtardasu abubuwan dake tafiya.
Mata ma suna taka rawa akungiyar maharban domin dasu aka fafata da mayakan Boko Haram. Wata cikinsu tace bata ci dadin abun da ya faru ba. Ta ba iyayen kasa hakuri da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5