An Samu Bayanai Masu Karo Da Juna Akan Yawan Mace-mace A Kano

Yayin da ake samun bayanai masu karo da juna game da musabbabin yawan mace-macen mutane a Kano, kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar Kano ya yi karin haske dangane da halin da wadanda suka kamu da cutar suke ciki bayan an killace su.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito shugaban kwamitin musamman da gwamnatin tarayyar Najeriya ta aika kan yaki da cutar coronavirus a jihar, Dr. Nasiru Sani Gwarzo na danganta yawan mace-macen mutane a ‘yan kwanakin nan a Kano da sabbabin cutar coronavirus.

Sai dai bayan sa’o’i kalilan, Dr. Nasiru Gwarzo ya musanta wadancan rahotanni yana mai cewa, kwamitin su na kwararraru na ci gaba da aikin bincike game da wannan batu, kuma nan bada jimawa zai wallafa rahotan sakamakon binciken.

Wakilin muryar Amurka ya yi kokarin samun Dr. Sani Gwarzo domin kara fayyacewa jama’a game da wadannan kalamai dake karo da juna kan lamarin mace-macen bil’adama a Kano, to amma lamarin ya ci tura.

Dr. Tijjani Hussaini, baboon jami'in kwamitin gwamnatin Kano na yaki da cutar coronavirus ya yi karin haske dangane da halin da mutanen da suka kamu da cutar suke ciki wadanda yawan su ya kai kusan 400.

Dr. Tijjani Hussaini ya ce, yawancin mutanen da aka killace basu da wata matsala suna cikin koshin lafiya, kuma a yanzu haka suna kokarin su sallami wadanda aka tabbatar da sun warke.

A jihar Jigawa kuwa a yau litinin, aka shiga rana ta uku da rufe wasu daga cikin kananan hukumomin jihar, saboda kaucewa yaduwar cutar coronavirus.

Dr. Abba Zakari dake zaman kwamishinan lafiya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar ya yi Karin bayani, inda ya ce, ana samun ci gaba sosai a jihar, domin mutanen da aka killace duka an gano wadanda suka yi mu’amala da su, kuma gwamnatin jihar tana kokarin rabawa al’ummar jihar kayan abinci, sannan al’umma jihar suna baiwa gwamnati hadin kai sosai.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Jigawa ke killace da almajirai su kimanin dubu daya, wadanda gwamnatocin jihohin Kano, Gombe da Nasarawa suka mayar dasu, amma gwamnatin jihar ta ce zata ci gaba da kula da almajiran sauran jihohi dake karatu a cikinta har zuwa lokacin gushewar annobar coronavirus.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Bayanai Masu Karo Da Juna Akan Yawan Mace-macen A Kano