An Sami Wasu 'Yan Australiya Da Kwayar Coronavirus

'Yan kasar Australiya su biyu wadanda da farko aka ce basa dauke da cutar Coronvirus bayan da aka yi masu gwajin cutar, yanzu an gano suna dauke da kwayar cutar bayan da suka dawo gida. Biyo bayan kebe su na sati biyu a jirgin ruwan shakatarwar nan na Diamond Princess da ya tsaya a Japan,

Brendan Murphy, babban jami'in kula da lafiya na Australiya ya ce "Zai yiwu a samu mutane da yawa na dauke da cutar bayan yin ingantaccen gwaji a 'yan kwanaki masu zuwa."

Sakamakon gwajin ya janyo tambayoyi game da ayyukan masu kula da lafiya na kebewa dake Japan.

A China, inda kwayar cutar ta fara bulla a karshen shekarar da ta gabata, adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar a yau Jumma'a ya karu zuwa 889, bayan da aka yi kwana biyu adadin masu kamuwa da cutar na raguwa.

A halin da ake ciki, Koriya ta Kudu a yau Jumma'a ta ba da rahoton cewa, sabbin wadanda suka kamu da cutar 52 ne, wanda ya kawo jimillar wadanda suka kamu zuwa 156.