Biyo bayan rantsar da sabbin ministoci a Najeriya matasa na ci gaba da maida martani. Sau da yawa dama matasan sun sha korafin cewa ba a damawa da su a harkokin gwamnati.
Sai dai ba haka matashi Abubakar Sadiq Umar, dan gwagwarmayar kwatowa matasa ‘yanci na kungiyar Kano State Youth Forum yake kallon wannan batu ba. A cewarsa wannan karon anyi kokari domin an nada matasan ministoci da suka cancanta.
Abubakar ya ce wannan batu da wasu matasa kan ce “duk wanda ya zarta shekaru 40 ya wuce zangon matashi” wannan batu ne na kanzon kurege domin a cewarsa matashin shekara 40 ya mallaki hankalinsa ya kuma fahimci mecece rayuwa.
Ya kuma ce a cikin jerin ministocin da shugaba Buhari ya nada, akalla akwai kimanin matasa 8 da suka cancanta wadanda zasu iya fitar da matasa kunya saboda irin kwarewarsu da gogewarsu da kuma zurfin karatun da su ka yi don tabbatar da ci gaban kasa baki daya.
Abubakar Ya kara jadadda cewar lokaci ya yi da matasa zasu farka daga baccin da suke yi su fuskanci rayuwa da kuma duba, shin wane matashi ne zai amfane su da wanda zai fitar da su daga kangin da suke ciki.
Your browser doesn’t support HTML5