WASHINGTON, D.C —
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya wato (NCDC), ta fitar da alkaluman sabbin kamuwa da cutar coronavirus (COVID-19) a kasar guda 195. Wannan ya kawo jimlar yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 1,728.
Sabbin alkaluman sun nuna cewa jihar Yobe ta sami mutum na farko da ya kamu da cutar.
Cibiyar ta ce an sami sababbin kamuwa 87 daga jihar Legas, 24 daga jihar Kano, 17 daga jihar Kaduna, 18 a jihar Gombe, 6 a Borno, 8 a Sokoto, 7 a Edo, 16 a Abuja, yayin da da jihohin Ebonyi da Adamawa su ke da guda dai-daya.
A cewar hukumar, yanzu haka Najeriya na da mutane 1,370 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 307 suka samu lafiya, sai mutane 51 da suka mutu.