WASHINGTON, D.C —
Gwamnatocin kasashen duniya suna yunkurin ɗaukar matakai don magance ɓarkewar cutar coronavirus dake yawan canjawa, wacce daga watan Disamba mutam sama da dubu dari da-goma-sha-takwas suka kamu da ita, sannan ta kashe kusan mutum dubu hudu da dari uku a kasashe dari-da-sha-hudu.
Kwayar cutar, wadda ake yi wa lakabi da COVID-19 a hukumance, ta fara bulla ne a China, inda jami'an kiwon lafiya a yau Laraba suka sanar da samun sabbin wadanda suka kamu da ita su ashirin da hudu.
Yayin da hakan ke nuna ana ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da cutar a China, kasar da yanzu ta dakatar da zirga-zirgar mutane a biranenta don hana yaduwar cutar daga wannan al’umma zuwa waccan, yanzu kuma ta na fama ne da karuwar sabbin masu dauke da cutar da ke zuwa daga wasu kasashe.
Hakan ne ya sa, jami’ai a Beijing suka ba da umarnin killace duk wanda ya shiga kasar na tsawon kwanaki 14.