An Sami Karancin Kifaye a Babban Tafkin Malawi

Masunta na fuskantar kalubalen rashin kifaye a Tafkin Malawi wanda shine tafki na uku mafi girma a Nahiyar Afirka.

Kasar Malawi na kokarin rage yawan kamun Kifin da ake yi a Tafkin Malawi, wanda shine tafki na uku mafi girma a Nahiyar Afirka. Tafkin ya zamanto wani babbar hanyar samun kudin shiga ga al’umomi masu tarin yawa da ke kewaye da tafkin.

Mazauna yankin sun ce rashin samun kifaye kamar yadda ake a baya da kuma sauyin yanayi sune suka haifar da matsalar da ake fuskanta. lamarin da ya sa masuntan ke neman mafita ta wasu hanyoyin.

Da yammacin kowacce rana, tarin masu sana’ar sayar da kifi kan taru a bakin tekun yankin Makawa suna jiran kifi daga masuntan, amma da yawa daga cikinsu na dawowa gida babu kifi saboda karancin kifin da ake fuskanta.

Wani masunci, Michael Makwinja ya ce “Misali kamar yau kam mafi yawanmu da muka je kamun kifi munyi asara sosai, inda mu ka koma gida da kashin da bai wuce wanda ya kai na kudin Malawi 2,000 ba, kwatankwacin dala 2. Wannan babbar asara ce a gare mu."

Masuntan sun daura alhakin rashin kifin kan sauyin yanayi, a yayin da wasu ke ganin karin yawan jiragen da aka saka a tafkin sune suke haifar da karancin kifin.

Hakan ya sa irin su Lucia Amidu su ka ninka kudin da sayar da kifayensu.

Ta ce a duk lokutan da suka samu kifi kadan, sukan sai da kireti daya akan kudin Malawi 70,000, (kusan dala 100), amma idan aka nema ragi, su kan sayar akan kudin Malawi 65,000 kwatankwacin dala 90. Amidu ta kara da cewa hakan na janyo musu faduwa har ma ya kai da, mun kasa ciyar da iyalinmu.

Karancin kifayen ya sa wasu masu sana’ar kifi irin su bar sana'ar su nema wata mafita ta daban, kamar irin su Joseph Maida, wanda ya koma harkar kiwon dabobi.

Ya ce "Kamar kashe tsuntsaye biyu ne da dutse guda, yanzu haka ina amfani da kashin dabbobi na wajen samar da taki, sannan yayin da na yi rashin kudi na kan yanka akuya daya don na sayar da naman.

A gefe guda kuma gwamnati na kokarin wayar da kan al’umma kan dokokin da zasu rage yawan kamun kifin. Wannan ya hada da hana yin amfnai da wasu ragar kamun kifi, da kuma hana kafin miki daga 'daya ga watan Nuwamba zuwa 3f1 ga watan Disamba.