An Sami Bullar Cutar Sankarau A Jamhuriyar Nijar

Rigakafin Cutar Sankarau A Afirka

An sami bullar cutar sankarau a Nijar har wasu sun rasu. Sai dai hukumomin kiwon lafiyar kasar sun ce suna iyakar kokarinsu na ganin sun shawo kan lamarin cutar.

Hukumomin kiwon lafiyar al’umma a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da bular cutar sankarau a kauyen Unguwar Malam dake gundumar Murya a yankin Zindar. Inda kuma tuni aka dauki matakin killace kauyen da wannan annoba ta shafa don kaucewa bazuwar kwayar cutar zuwa wasu sassan kasar.

Wannan sanarwa ta fito ne daga taron manema labarai da mahukunta suka yi don jan hankalin jama’a ta bakin Magatakardar Ministan Lafiya Malam Ranau Abashe, tare da tabbatar da cewa har ma cutar ta sankarau da har mutane arba’in sun kamu har daya daga cikinsu ya rasu.

Ya bayyana cewa sauran mace-macen da ake cewa an samu kamart mutane goma sha biyu sun mutu kafin su hukumar lafiya ta sami labara ko kuma isa wajen da aka ce abin ya shafa. Ya kuma tabbatar da cewa sun tanadi magunguna tare da alluran rigakafi.

Bugu da kari kuma su wadanda aka samu da ciwon an killace su don kar su harbawa jama’ar da ke da lafiya. Daga watan Janairu zuwa na Afrilun shekarar 2017 a fadin kasar Nijar, kimanin mutane dubu biyu da dari daya ne dai suka kamu da cutar tare da rasa ran akalla dari da ashirin daga cikin mutanen.

Ga cikakken rahoton Wakilinmu Sule Mumuni Barma cikin muryar daga Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

An Sami Bullar Cutar Sankarau A Jamhuriyar Nijar - 2:48