A cikin wani rohoto da Stacey Knott ta ruwaito daga birnin Cape Coast, ta ce yara a kasar Ghana sun fara samun sabon maganin rigakafin da aka yi don dakatar da cutar cizon sauro wato malaria.
Kasar Ghana ita ce kasa ta biyu a Afrika, da ta sami maganin rigakafin, wanda ake sa ran zai rage yawan kamuwa da cutar ta cizon sauro da wani lokaci take kisa. Amma masana sun yi gargadin cewa har yanzu sauran matakan kare kamuwa da cutar suna da muhimmanci.
An kwashe fiye da shekaru 30 da kusan dala biliyan 1 ana hada maganin rigakafin da aka kaddamar a kasar Ghana yau Jumma'a.
Maganin rigakafin, wanda ake kira RTS-S, yana rage yawan yaduwar cutar cizon sauro a yara da kusan kashi 40.
Kasar Ghana, da Kenya, da kuma Malawi su na cikin kasashen da zasu fara karbar shirin gwajin rigakafin, wanda aka fara a makon da ya gabata a kasar Malawi. Ana sa ran a cikin shekaru hudu masu zuwa, kimanin yara miliyan daya zasu sami rigakafin na RTS-S kashi hudu.
Babban birnin Cape Coast na daya daga cikin yankuna uku na kasar Ghana da aka maida hankali akai saboda yadda ake yawan samun cutar malaria a yankin.
Alurar rigakafin na zaman wani karin mataki na yaki da cutar, da kuma gidajen sauro da maganin feshin kwari a cikin gida da ake amfani da su.
Richard Mihijo, jami'in hukumar kula da lafiya ta duniya, ya ce ana bukatar maganin rigakafin saboda kokarin da akayi na yaki da cutar ya ci tura a cikin 'yan shekarun nan.