An saki tsohon shugaban asusun lamuni na Duniya Dominque Strauss-Kahn

Tsohon Shugaban asusun bada lamuni na duniya, Dominique Strass-Kahn.

Wani alkali a birnin New York ya saki tsohon shugaban asusun bada lamuni na duniya Dominique Strauss-Khan ba tare da bukatar beli ko daurin talala ba dangane da tukumarshi da da ake yi bisa zargin neman yin lalata da wata mace ba tare da izininta ba.

Wani alkali a birnin New York ya saki tsohon shugaban asusun bada lamuni na duniya Dominique Strauss-Khan ba tare da bukatar beli ko daurin talala ba dangane da tukumarshi da da ake yi bisa zargin neman yin lalata da wata mace ba tare da izininta ba. Alkalin ya yanke shawarar sakinshi ne bayanda masu shigar da kara suka bayyana tababa game da gaskiyar macen da ta zargi Strauss-Kahn da kai mata hari. Ba a yi fatali da ko daya daga laifukan da ake tuhumarshi da aikatawa ba, kuma masu shigar da kara sun ce zasu ci gaba da gudanar da bincike. Ba a mayarwa Strauss-Kahn da takardar Paspo dinshi ba, saboda haka ba zai iya komawa kasarshi Faransa ba. An kama tsohon dan siyasar kasar Faranshin ne aka kuma tuhume shi da kaiwa wata mace ‘yar shekaru 32 ma’aikaciya da ta je share mashi dakinshi a wani otel din kawa dake birnin New York. Jaridar NY Times tace macen da ke zarginshi, ‘yar asalin kasar Guinea, ta yi ta shantalawa masu shigar da kara karya tun daga lokacinda ta yi zargin. Jaridar tace an sami sabanin gaske game da asalin matar, wadda ya hada da takardar neman mafaka da ta rubuta, da kuma alaka da wadansu miyagun ayyuka da suka kunshi safarar miyagun kwayoyi da kuma batad da sawun kudin haram. Strauss-Kahn ya musanta aikata wannan laifin. Alkalin ya maidawa Strauss-Kahn dala miliyan shida kudin belin day a biya aka kuma sake shi daga daurin talala.