An Saki Sambo Dasuki

Kanar Sambo Dasuki

Zan ci gaba da zuwa kotu don kare kaina, akan laifin da ake tuhuma ta da shi wanda ban aikata ba.

Hukumomin Najeriya, sun saki tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa a fannin tsaro, Kanar Sambo Dasuki.

A daren yau Talata ne dai Hukumar Tsaro ta Farin Kaya SSS a Najeriya, ta ba da belin Dasuki, wanda ya yi aiki karkashin gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan.

Da safiyar yau gwamnatin tarayyar ta sanar da cewa ta ba da umurnin a saki Dasuki, kamar yadda Ministan Shari'a Abubakar Malami ya tabbatar.

Mohammed Sambo Dasuki

Kanar Sambo Dasuki, dai ya kwashe fiye da shekara hudu yana tsare, inda ake tuhumar shi da laifin almubazzarancin wasu makudan kudade, da aka ware don sayo makaman yaki da kungiyar Boko Haram.

Jim kadan bayan sako shi, Dasuki ya nuna farin cikinsa a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

Sambo Dasuki

“Babu wani abu da zan yi amfani da shi wajen bayyana farin cikina ga Allah, da kuma jama’ar kasa da suka taya ni da addu’a, wannan wata muhimmiyar rana ce gare ni da ma iyalaina.”

Ya kara da cewar, babu wani rashin jituwa tsakaninsa da shugaba Muhammadu Buhari, kuma zai ci gaba da bibiyar wannan zargin da ake yi mishi a kotu.

Tuni dai tsohon mai ba da shawara a fannin tsaron na Najeriya ya tabbatarwa da VOA cewa, ya koma cikin iyalansa, inda ya kara da cewa, "ina cikin koshin lafiya."

Shi ma tsohon gwamnan jihar Sokoto Alh. Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yaba da sakin Dasuki da aka yi.

Saurari tattaunawar ma'aikacin Muryar Amurka Yusuf Aliyu Harande da Kanar Sambo cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Saki Sambo Dasuki 2'20"