An Saki Hinckley,Mutuminda Ya Harbi Ronald Reagan A 1981.

John Hinckley Jr yayinda ya isa wata kotun Amurka a shekaru ta 2003.

Kotu bata Hinckley laifi kan harbin tsohon shugaba Reagan ba, bisa dalilai na rashin koshin hankali.

Asabar din nan ake sa ran hukumomin Amurka zasu saki John Hinckley, mutuminda yayi yunkurin kashe shugaban Amurka Ronald Reagan shekaru 35 da suka wuce.

Hinckely,wanda yake wani asibiti na masu tabin hankali anan birnin Washington, sakin nasa na har abada ne, bayan da wani alkali ya yanke hukuncin cikin watan Yuli cewa, Hinckley ba zai kasance barazana ko hadari ga kansa ko al'uma ba.

Hinckley, zai zauna da mahaifiyarsa 'yar shekaru 90 da haifuwa, a unguwar da ake kira Williamsburg, a yankin da gidajen suke akillace, a jahar Virginia. Inda zai zaunan, yana da nisan kilomita 250 kudu maso gabashin birnin Washington DC. Sakin nasa yana dauke da sharudda masu yawa.

Dan shekaru 61 da haifuwa, sakin Hinckley, ya biyo bayan shekaru masu yawa yana jinya a wani asibiti da ake kira St. Elizabeth na tsawon shekaru fiyeda 30, bayan kotu ta wanke shi daga zargin harbin tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan da wasu mutane uku, bisa dalilan bashi da cikakken hankali.

Hinckley, ya fara kiwon Reagan, daga bisani ya harbe shi, tareda sakataren yada labaransa James Brady, da wani dogarin shugaba Reagan, da kuma wani dan sanda a harabar wani O'tel anan birnin Washington DC a shekarar 1981. Sakataren yada labarai Brady, ya sami nakasa a kwakwalwa kuma ya mutu a shekara ta 2014.

Tsohon shugaban Amurka Reagan, shi da sauran wadanda aka harba sun warke daga harbin.
A shekara ta 2004 ne Allah Ya yiwa Ronald Reagan rasuwa.