An Saki Madugun Adawar Kasar Kamaru

An saki madugun babbar jam’iyyar adawar kasar Kamaru Maurice Kamto a jiya Asabar bayan da wata kotun soja ta ce a sake shi bisa umurnin shugaba Paul Biya.

An saki madugun adawar ne bayan ya kwashe watannin 9 a gidan yari kuma bayan da shugaba Biya ya nuna alamun neman sasanchi na ba-zata, shugaban da ke fuskantar tarin korafe-korafe daga kasar da kuma suka daga kasashen waje akan ‘yancin siyasa.

“Ga mu nan mun hadu a yau, na gode da goyan bayan da kuka bani ba kakkautawa,” abinda Kamto ya fadawa daruruwan masu goyon bayansa kenan da suka tarbe shi. Ya ce na ga abinda kuka yi duk da cewa ba ku iya gani na ba.”

Kamto ya sanar da sake bude wani sabon babi a gwagwarmayar da yake yi, ya kara da cewa idan wasu mutane na tunanin cewa ‘yantar da mu na nufin karshen gwagwarmaya to basu fahimci komai ba.”

An kama Kamto dan shekaru 65 da haihuwa a karshen watan Janairu bayan watannin da aka kwashe ana zanga zanga akan sakamakon zaben da aka yi a watan Oktoba na shekarar 2018.

Biya dan shekaru 86 da haihuwa, wanda kusan shekaru 37 kenan yana mulkin kama-karya a Kamaru, ranar Jumma’a ya sanar da cewa ya bada umurnin a yi watsi da zarge-zargen da ake yiwa wasu shugabannin ‘yan adawar kasar, ciki har da wasu da yawa daga jam’iyyar MRC wadda Kamto ke jagoranta.