An Saki Alaramma Bayan Kotu A Saudiyya Ta Wanke Shi Daga Zargi

Alaramma Ibrahim Ibrahim

Wata kotu a Saudiyya ta wanke wani dan Najeriya Alaramma Ibrahim Ibrahim daga zargin da aka yi masa na shiga kasar da kwayoyi. An sake shi ne bayan da kotu a Saudiyyar ta wanke shi. Ya shafe shekaru uku a tsare.

Shugabar hukumar kula da kadun 'yan Najeriya a ketare, Abike Dabiri Erewa, ta tabbatar da sakin Sheikh Ibrahim Ibrahim a shafinta na twitter.

Sheikh Ibrahim, wanda ya tafi Umrah a 2017 ta filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ya hadu da wannan ibtila’in ne yayin da aka ga wata jaka da kwayoyi da a ke zargin shi ne ya shigowa da ita.

A zantawar da wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu el-Hikaya, ya yi da Sheik Ibrahim ta wayar tarho, ya ce ya dage ne da addu'a don kubuta daga tuhumar mai daukar hukuncin kisa.

Alaramma Ibrahim Ibrahim

Wasu malaman addini sun ja hankalin gwamnatin Najeriya don sanya baki a lamarin, inda Ministan shari'a Abubakar Malami ya dauki matakai.

Alkassim Yawuri shi ne sakataren Jam'iyyatu Ansarul Din Attijjaniyya, ya bayyana kokarin da su ka yi na jan hankalin dukkan hukumomin da lamarin ya shafa don ceto Malam Ibrahim.

A baya an samu wata 'yar Najeriya da ta kubuta daga irin wannan tuhuma bayan cusa ma ta kwaya da gangan a jakarta.

A saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

KOTU TA WANKE IBRAHIM IBRAHIM