Ana Kan Yinkurin Sake Hada Kan Bangarorin Izala Wuri Guda

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya (Bangaren Kaduna), Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya (Bangaren Kaduna), Sheikh Abdullahi Bala Lau.

A ci gaba da tabbatar da kwanciyar hankali da shugabannin al'umma ke yi albarkacin lokacin da ake ciki na yawaita ayyukan alkhairi, wasu magabata na wata hobbasa ta sake hade bangarorin kungiyar Izala ta Najeriya wuri guda.

Bayan share Shekaru da dama da darewa gida biyu na kungiyar Izalatul bid’ah wa ikamatus sunnah, wadda aka fi kira ‘Izala,’ kawai mai wa’azin addinin Musulunci a Nigeria dama wasu kasahen Afurka ta Yamma, wato da Bangaren ‘Yan Kaduna da Sheik Abdullahi Bala Lau ke Shugabanta da Kuma Bangaren ‘Yan Jos da Sheik Sani Yahaya Jingir ke shugabanta, a yanzu an sake wani yinkuri na hade kan bangarori yayin da ake daukar matakai iri iri masu fa’ida a wannan wata mai tsarki na Ramadan.

Idan an tuna dai, bayan rabuwar kungiyar ta Izala a shekarar 1991 an yi nasarar sake hade ta wuri guda a shekarar 2011. Amma tafiyar ba ta yi nisa ba, ko wane bangare ya kama gabansa, To sai dai ko ma bayan nan, wasu bayin Allah sun yi ta kokarin hada kan jama’a. Amma watakila saboda ganin nasarar da aka yi a baya ta hade kan kungiyar ba ta dore ba, wannan karon an yi ta bi sannu a hankali har sai da Allah ya kawo al’amarin ga wannan mataki.

Wato, a yanzu dai wasu manyan masu fada aji ne na bangarorin biyu na izalar su ka fara wannan yinkuri na yanzu na sake dunkule Izalar wuri guda. Kan wannan hobbasar, Sheik Dr.Abubakar Giro Argungu, wanda shi ne shugaban Kwamitin Ayyuka na Kungiyar Izalar Najeriya Mai hedikwata a Abuja fadar Gwamnatin Nigeria, ya yi bayani kan wannan yinkuri na baya bayan nan da kuma yadda su ke kallon al’amari cike da kyakyawan zato.

Shi ma Dr.Mustapha Basher Babban jigon Izalar ta Bangaren Jos, kuma Shugaban Iheyaussunnah a kasar Janhuriyar Nijar, wanda a yanzu haka yake tafsirin Ramadan a jihar Nejan Nigeria, yace suna da kyakkyawan zato akan wannan yunkuri. Ya na mai bayyana dalikansa.

A yanzu dai lokaci ne zai nuna ko haka zata cimma ruwa a wannan yunkuri na baya bayan nan.

Saurari rahoton Mustapha Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Yinkurin Sake Hade Kungiyoyin Izala Wuri Guda