Wani jami'in 'yan sandan jihar Adamawa ya yiwa wakilin Muryar Amurka dake Yola, Ibrahim Abdulaziz, bayanin abubuwan dake faruwa.
Dangane da matakan da suka dauka a matsayinsu na jami'an tsaro ya ce sun baza mutanensu a duka kauyukan da aka kai hari da kewayensu. Ya tabbatar da samun labarin barkewar rikici a kauyen Dung dake cikin karamar hukumar Demsa. Ya ce hankulan sojojin sama da na kasa da 'yan sanda sun koma yankin. Injishi sun dauki duk matakan tsaron da suka kamata su dauka. Ya kara da kiran jama'a da su daina yin aiki da jita jita saboda wai sun samu wasu rahotanni amma da suka duba lamarin sai ya kasance sabanin abun da aka gaya masu.
A kan ko rayuka nawa suka salwanta jami'in tsaron ya ce bashi da labari. Sai dai ya yi alkawarin bada duk wani karin bayani da suka samu nan gaba.
Dangane da labarin cewa an tare hanyar zuwa Gombe daga Yola ana tsayar da motoci ana kashe mutane, jami'in ya karyata batun. Ya ce babu gaskiya ciki saboda motocinsu suna sintiri akan hanyar. Bugu da kari, sun kara jami'an tsaro a hanyar. Suna kuma jaddadawa jami'ansu su tabbatar ba'a samu irin wannan lamarin ba a hanyar.
Akan Savana tare da cewa an kona kamfanin Savana, har wa yau jami'in ya ce duk jita jita ne saboda akwai jami'ansu da yawa a yankin Savanan.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5