Shugaban kasar Sudan Umar Albashir wanda kotun kasa da kasa dake birnin Hugue ke nema akan laifin yaki, an sake rantsad dashi a matsayin sabon shugaban kasar a jiya Talata.
Al-Bashir zai sake kwashe wasu shekaru 5 a matsayin shugaban kasar ta Sudan. Yayi alkawarin zai yaki cin hanci da rashawa kana ya inganta tattalin arzikin kasar sailin ya dawo da zaman lafiya a yammacin kasar.
Haka kuma yayi alkawarin samar da zaman lafiya a sassan kasar uku masu kokarin ganin sun kifar da gwamnatin sa da suka hada da yankin Dafur, Kordofan da kuma yankin kogin Nilu.
Shugaba Al-bashir ya jaddada ahuwa ta dindindin ga dukkan dan tawayen da ya ajiye makaminsa domin shiga sulhu.
Shi dai Al-Bashir yamulki sudan har na tsawon shekaru 26, wadda yaki bai dai daita ta ba sai dai kam tasha yawan takunkunmi daga kasashen duniya a lokutta daban-daban, wanda har hakan yasa tayi babban hasarar samun kudin shiga na kasuwancin mai