An Sake Rage Farashin Man Fetur a Najeriya

Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur da kayyade farashi ta PPPRA a Najeriya, ta sanar da rage farashin man fetur a kasar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar wacce babban jami'inta Abdulkadir Sa'idu ya sanya wa hannu, hukumar ta ce an mayar da farashin na mai zuwa naira 123 da kwabo 50 kan kowacce lita.

Za a fara amfani da wannan farashin ne daga ranar 1 ga watan Afrilun shekarar 2020.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan, bayan da aka sanar da rage farashin man fetur daga naira 145 zuwa naira 125 kan kowacce lita.

Sanarwar ta kuma ce hukumomin da ke da ruwa da tsaki kan harkar mai za su sa ido domin tabbatar da an bi wannan sabon farashi da aka saka.