An Sake Bude Wuraren Ibada A Kaduna

  • Murtala Sanyinna

GWAMNA Nasir El RUFAI

An bude wuraren Ibada a Kaduna bayan da suka kasance a rufe tsawon watanni hudu sakamakon annobar coronavirus

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana bude wuraren ibada na Musulmai da Kirista, bayan rufe su watanni 4 da suka gabata sakamakon annobar coronavirus.

A can baya dai gwamnatin ta rurrufe kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a, ciki har da masallatai da majami’u, a matsayin wani sashe na matakan dakile yaduwar cutar.

To sai dai a makon jiya gwamnatin ta kira taron manyan malaman addinin Musulnci da na Kirista, domin tattauna yadda za a bude masallatai da majami’un da ke fadin jihar don gudanar da ibada ta yau da kullum.

Shugaban hukumar kula harkokin addinin musulunchi da Kirista a jahar Kaduna, Sheik Jamilu Abubakar Albani, ya ce za’a bude guraren ibadar ne bayan cimma matsaya da kafa sharudan ci gaba da kiyaye yaduwar cutar ta coronavirus a jihar.

Wannan matakin na bude guraren ibada ya yi wa shuwagabannin addini da mabiyansu dadi.

Shugaban kungiyar Kiristochi ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna Rev. Joseph John Hayep, sa sakataren Majalissar malamai da limamai ta jihar Kaduna Malam Yusuf Yakub Arrigasiyyu, duk sun yabawa gwamnati da daukar matakin, kana kuma suka yi kira mabiyansu da su tabbatar da daukar matakai da sharudan da aka gindaya domin kaucewa dawowar yaduwar cutar ta coronavirus.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Kaduna Isah Lawal Ikara ya ce ya zuwa yanzu, makarantu ne kadai za’a iya cewa ba’a kai ga budewa ba a jihar, domin ko a makon jiya sai da gwamnatin Kaduna ta bude babbar kasuwar jihar tare da alkawarin bude sauran kasuwanni sannu a hankali.