An Sake Arangama Tsakanin Masu Zanga Zanga Da 'Yan Sanda A Hong Kong

Masu zanga-zangar goyon bayan dimokradiyya a Hong Kong sun yi arangama da ‘yan sandan yankin a yau Asabar a yayinda masu zanga-zangar suka hau kan tituna makonni 13 kenan a jere suna bijirewa dokar haramta zanga-zangar da gwamnatin Hong Kong ta sanya.

‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa, da wasu motoci masu feshin wani ruwa mai launin bula akan masu zanga-zangar a gaban ginin majalisar dokokin yankin, don su iya gane su da sauri. Masu zanga-zangar sanye da bakaken kaya, sun yi ta jifar ‘yan sandan da duwatsu da kuma wasu ababen fashewa a yayinda su kuma suka dinga kare kansu da lemomin da suka rike.

An ga hayaki ya turnike wata babbar marabar hanya a kusa da helkwatar ‘yan sandan Hong Kong bayan da masu zanga-zangar suka bankawa wani shinge wuta.

An dai iya kashe wutar yayinda ‘yan sanda suka kora masu zanga-zangar cikin wani rukunin kasuwanni da shaguna a birnin Hong Kong inda suka harba masu barkonon tsohuwa, jefi-jefi kuma suka harba masu harsasan roba.