Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi al’ummar jihar da su guji yada jita jita don gujewa dukkannin wani tashin hankali da ka iya tayar da zaune tsaye.
WASHINGTON, DC —
Da yake jawabi gaban manema labaru mataimakin gwamnan Barnabas Bala Bantex, yace gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya faru a masarautar
Godogodo a karamar hukumar Jama’a dake kudancin jihar Kaduna, wanda ta kawo sanadiyyar rasa rayuka da kuma asarar dukiyoyin jama’a.
Tuni dai karamar hukumar Jama’a dai ta sanya dokar hana yaw ta sa’o’i 24 a cewar kantoman riko na karamar hukumar Dakta Bege Katika.
Rahotanni daga yankin dai na cewa an ga mutane na guje guje biyo bayan tashin hankalin, yayin da aka ce abin ya rutsa da wasu wadanda suka je wucewa.
Saurari cikakken rahotan Isah Lawal Ikra daga Kaduna.
Your browser doesn’t support HTML5