An sace wani dan jarida ma’aikacin gidan talabijin mai zaman kansa mai suna Goobjoog inda aka ritsa shi da bindiga a wajen birnin Mogadishu bayan barazana da yayi ta fuskanta ta hanyar wayar tarho, cewar Matarsa.
WASHINGTON, DC —
Mai shirya labaran talabijin Hanad Ali Guled yana kofar gidan sane a hanyar sa ta zuwa wajen aiki yayin da wasu yan bindiga rufe da fuskokin su suka dauke shi a safiyar Asabar din nan.
Wani Editan tashar Radiyo mai suna Ahmedwali Hussein yace Guled ya kira iyalinsa daga wata lamba da ba’asan daga inda ya kiraba yace ana azabtar dashi.
A wani bayani na shafin yanar gizon Goobjoog yace barazanar da Guled yake samu na da alaka ne da aikin sa akan kamfe na samar da sauki akan fari. Guled shi ya kafa kungiyar da ake kira Media for Aid, wani shiri da yake karawa mutane karfin gwiwa don tallafawa wadanda fari ya shafa.
Har izuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin sace Guled, Goobjoog na kira da asake shi nan take.