A jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, wani babban jami'in dan sanda mai kula da yanki, wato “Area Commander" ACP Abdullahi Umar Kamba ya fada hannun masu garkuwa da mutane.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da dare a wani gari da ake kira Tashar Rogo a kusa da garin Yauri, a lokacin da jami'in dan sandan ke tafiya tare da iyalinsa cikin mota.
Nan take dai rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi bata ce komai ba game da batun.
Wani na kusa da jami'in da aka sace ya shaida wa Muryar Amurka cewa ACP Abdullahi ya tabbatar masa halin da yake ciki ta waya ranar Juma'a da safe, amma masu garkuwar ba su tafi da matarsa ba.
A jihar Sokoto da ke makwabtaka da jihar ta Kebbi, jama'a na cikin halin rashin tabbas dangane da sha'anin rashin tsaro, domin ko a daren Alhamis a wannan makon an kai hari a wani gari da ke Illela.
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Illela, Bello Isa Ambarura, yace duk da yawan jami'an tsaro da ke kan hanyar Illela barayi na ci gaba da kai wa jama'ar yankin hare-hare.
Ya kara da cewa kwana biyu da suka wuce 'yan bindiga sun kai hari a wani gari mai suna Kalaba, inda suka sace mutane uku. Bayan haka a ranar Alhamis maharan sun sake kai hari a wani gari da ke yankin Darna Tsaulawo inda suka kashe mutum biyu suka kuma sace wasu biyar.
A baya, ‘yan banga kan taimaka wajen tsaron jama'a amma yanzu abin ya fi karfinsu, duba da yadda barayin ke zuwa da yawa dauke da manyan makamai.
A kan batun rashin tsaro dai ‘yan Najeriya na ci gaba da zura ido su ga yadda Allah zai yi, domin matsalar ta ki karewa duk da kokarin da mahukunta ke cewa suna yi.
Saurari rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5