'Yan sa'o'i kawai bayan da yarjajjeniyar zaman lafiyar da Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir da 'yan tawaye su ka cimma ta fara aiki an saba ma ta; kuma kowane bangare na zargin dayan da fara kai hari a wannan kasar ta yankin tsakiyar gabashin Afirka.
Mai magana da yawun 'yan tawaye Lam Paul Gabriel ya zargi sojojin gwamnati da kai hari kan dakarun 'yan tawaye a bayan birnin Wau, bayan sa'o'i shida kawai da yarjajjeniyar ta fara aiki.
Shi kuma mai magana da yawun gwamnati Ateny Wek Ateny, ya gaya ma kamfanin dillamcin labarai na Associated Press cewa 'yan tawayen ne su ka fara kai hari har su ka nemi uzuhuri bisa hujjar cewa, "Ba su da kintsattsan jagoranci. Ba su kuma da takamaiman shugaba."