Hukumar shige da ficen Najeriya sun rufe kan iyakokin Najeriya ciki har da Kamaru biyo bayan shirin gudanar da babban zaben kasar a gobe 28 ga watan Maris din gobe. Wakilin Muryar Amurka a Kamaru Mamadou Danda ya yiwa Mahmud Lalo bayanin yadda abin yake ta wayar tarho.
Danda yace, “Game da rufe iyakar da aka yi tsakanin iyakar Kamaru da Najeriya dama abune wanda baya tada hankali, tunda dama ‘yan kasuwa tuni suna kaiwa da kawowarsu a yanki. Sannan akwai wuraren da ba yadda za’a yi a iya tsare wajen gaba daya.
Ya kara da cewa ko yau yaga wasu da Babura sun shiga ta wasu hanyoyin ratsen da ba makawa karya doka ne. Wasu abubuwan masarufin da ake shige da ficensu abun bukata ne ba yadda suka iya.
‘Yan kasar Kamarun dai sun nuna cewa in Najeriya ta dage da yin zaben da ba magudi balle ayi tashin hankali to hakan zai haifar da da mai ido ga kasar da ma makotanta.
Your browser doesn’t support HTML5