An Rufe Asibitoci da Makarantu a Nijer

Kakakin Majalisa jamhuriyar NijerHama Amadou.

‘Yan siyasa sun fara maida martani akan kiraye-kiraye da kungiyoyin fararen hula suka sha yi masu dangane da halin rudanin siyasar i.
Kungiyoyin fararen hula a kasar Nijer sun yi kira ga ‘yan siyasar kasar dasu maida hankali akan halin da kasar ke ciki masammam bukatocin talakawa da suke fama dasu.

Ba gardamar siyasa ba, wanda idan hakan ya ci gaba ba zai haifarwa jamhuriyar Nijer dan mai ido ba.

Abdulmumini Usman kakakin kungiyoyin fararen hula Nijer,yace “basu tunanin kasar Nijer,tunanin junarsu sukeyi,daga yau kowa ya kama jikin shi mace da namiji kowa yayi tsaye yace lallai kasar nan don goben ta yakamata mu kama jikin mu,yau ka duba ka gani man fetur ake hakowa wake ci albarkan shi, ana zancen Yureniyam kana gani zinari aka samu ana cewa kada talakawa suje.”

Ya kara da cewa “ ka duba kaga kasar nan sai karban bashi amma ba’a ganin amfani bashi,makarantu da asibitoci suna rife kasa ta tsaya,lokaci da aka ce an kawo dubunnan miliyoyi cikin kasar gashi kasar tayi tsaye,yace tsayawa za’a yi ana kallon su.”

Tuni dai ‘yan siyasa suka fara maida martani akan kiraye-kiraye da kungiyoyin fararen hula suka sha yi masu dangance da halin rudanin siyasar da ake ciki.

Wani dan majalisa bangaren masu mulki,Asmanu malam Isa cewa yayi wannan kiran da suka yi kira ne mai mahimmaci kuma yakamata ‘yan siyasa su saurare shi.

Alhaji Lawali Leje shine kakakin ‘yan adawa,” yace inda aikin na tafiya dai-dai ai fararen hula baza suyi wannan furuci ba.

Your browser doesn’t support HTML5

An Rufe Asibitoci da Makarantu - 2'45"