An raunana mutum hudu a birnin Minna jihar Niger a sakamakon rikicin addini

Wani Masalaci

Mtum hudu sun ji rauni, kuma a lalata dukiya da yawa a birnin Minna jihar Niger a sakamakon rikicin daya barke tsakanin yan Darika da yan Izala

Wakilin sashen Hausa a Minna Mustapha Nasiru Batsari ya aiko mana da rahoton cewa an raunana akalla mutane hudu da lalata dukiya da yawa a birnin Minna jihar Niger a daren Juma'a, a sakamakon rikici daya barke tsakanin yan Darikar da yan Izala.

Wannan rikici kuwa ya faru ne a saboda kokarin mallakar wani Masalaci kusa da gidan sarkin Minna.

Mallam Sani Abubakar dake bangaren kungiyar Izala, yace mutum hudu aka jiwa rauni. Yace wasu sun gudu a saboda halin da ake ciki.

Shi kuma Mallam Bala Jibiril Limamin gidan gwamnatin jihar Niger, yace maharan sun zo ne da bam din da ake hadawa da kwalabe da petro, suka dinga jefawa mutane. Suka shiga gidan wani mutum suka kona, Sa'anan suka shiga shaguna mutane suka kona.

Sheikh Abubakar yace halin da ake ciki a yanzu a Nigeria, ba'a bukatar duk wani rikicin addini. Ana kokarin shawo kan matsalar yan Boko Haram, bai kamata a hadasa wata sabuwa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

MINNA MOSQUE ATTACK