Ya yin da ‘yan Najeriya ke ficewa daga kasar zuwa wasu kasashe domin samun sabuwar rayuwa da zama ‘yan wasu kasashen, sai ga shi wasu ‘yan kasashen waje ne ke zama ‘yan Najeriya.
Ya zuwa yanzu dai ‘yan wasu kasashen da suka hada da Indiyawa da ‘yan Pakistan da Lebanon da kuma wasu ‘yan kasashen Afirka kimanin su 335 suka zabi zama ‘yan Najeriya domin gashin kansu.
A wani biki da aka gudanar a birnin Abuja, Ministan cikin gida Janar Abdurrahman Dambazau, ya bukaci sabbin ‘yan Najeriyan da su kasance masu biyayya ga tsarin mulkin ‘kasa da kuma ci gaba da bayar da gudunmawarsu ta fuskoki daban-daban.
Da yake jawabinsa ga sabbin ‘yan Najeriyar, Dambazau, ya ce bayan cika ka’idoji da tsarin mulki ya tanadar shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya amince da bukatarku ta zama ‘yan Najeriya.
Zama ‘dan wata ‘kasa dai ba bakon abu bane a kasashe daban-daban na duniya, wadanda ake karuwa walau ta fuskar kasuwanci ko basirar da bakin ke kaiwa sabuwar kasar ta su.
Domin ‘karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5