An Rantsar Da Hassan Muhammad a Matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Bayan Tsige Gusau

Zauren Majalisar dokokin jihar Zamfara (Hoto: Instagram/Joe AH.Ali Photography)

'Yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Gusau, Sanata Hassan Muhammad kuma ya maye gurbinsa.

Ranar Laraba 23 ga watan Fabarairu ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara suka tsige Mahdi Gusau mataimakin gwamnan jihar a lokacin wani zama jim kadan bayan da majalisar ta karbi rahoton kwamitin da babbar mai shari’ar jihar Justice Kulu Aliyu ta nada, don yin bincike akan mataimakin gwamnan, a cewar gidan talabijin din Channels a Najeriya.

Kwamitin mai mambobi bakwai da ya yi bincike akan laifuffukan da aka zargi Gusau da su, a karkashin jagorancin alkali Halidu Sabo mai ritaya, ya mika wa majalisar dokokin rahoton. Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Nasiru Mu’azu, shi ne ya karbi rahoton.

Daya daga cikin mambobin kwamitin Oladipo Okpeseyi, ya fada wa kakakin majalisar cewa kwamitin ya yi aikin da aka sa shi ya yi. Ya kuma fadi cewa ba su da hurumin bayyana wa wani abinda rahoton ya kunsa.

Mu'azu ya ce majalisar za ta yi aiki akan rahoton bisa ga tanadin kundin tsarin mulki.

A halin da ake ciki, an rantsar da Sanata Hassan Muhammad a matsayin mataimakin gwamnan jihar bayan da ‘yan majalisar suka tantance shi a zaman na ranar Laraba.