An gudanar da bikin ne a wurin da ake kira Palais des sports a ranar asabar karkashin jagorancin alkalan kotun tsarin mulkin kasa.
A matsayin damar bashi mulkin waadin shekaru 5, biyo bayan lashe zaben 20 ga watan maris da kashi 92.5i daga cikin 100 na kuriu.
A cikin jawabin sa shugaba Isoufu Muhammadu yayi bitar waadin mulkin sa na farko sailin nan yace zai kara kaimi zwajen yaki da taaddanci tare hadin kan kasashe makwabta.
Mallam Birjie Rafini shine Prime Ministan Niger.
‘’ALLAH ya kawo mu wannan rana mun gode masa kuma muna fata ALLAH sa shekaru biyar masu zuwa shugaba Muhammadu Isoufu ya samu ikon yin abinda yake fata ga kasar Niger, domin kunji a kunnen yadda yake son ya mayar da Niger ta zama kasa ce kyakkyawa kuma kasa mai albarka ta zama mai albarka wadda ALLAH ya kare ta da abubuwan gani akwai a ko ina cikin Niger.’’
Sai dai da wakilin Muryar Amurka ya tambaye ko me tsakanin gwamnati da ‘yan adawa.Ga kuma abinda yake cewa.
‘’Wannan abu mai wucewa ne domin kunji yace yana aikin gina kasa yana fata kowa da kowa yazo domin ya bada nasa gudun mowar.Hannun sa har yanzu a bude yake ga dukkan dan kasa mai kaunar kasar kuma yake son ayi wa kasar aiki. ’’
Shugabannin kasashen Africa 9 ne suka halarci bikin na rantsad da shugaba Muhammadu Isoufu galibin su makwabtar kasar ta Niger.
Ga Sule Mummuni Barma da ci gaban rahoton 4’52
Your browser doesn’t support HTML5