An Nemi 'Yan kasuwar Su Saka Hannun Jari a Kasuwar Dole Ta Damagaram

Wata kasuwar baje koli a Jamhuriyar Nijar

A Jihar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar, an nemi ‘yan kasuwa da su saka hannayen jari wajen gudanar da sabuwar kasuwar Dole domin su ma su amfana da ita.

Wani kamfani mai suna SOGEMAZ da aka kafa ne zai kula da tafiyar da sabuwar kasuwar zamani Dole ta Damagaram.

Kimanin miliyan 500 ake bukata don fara aikin a wa'adi na shekaru 20 a matakin farko.

“Ya kamata a ce ‘yan kasuwa na jihar Damagaram, ya zamanto su ne masu karfin jari a wannan kasuwa, don saboda su yi iko da kasuwar, shi ya sa aka bas u kashi 50 na wannan kasuwa.” Inji

Alhaji Laminu Ammani, babban darekta na zauren ‘yan kasuwa a jihar ta Damagaram.

Ya kara da cewa tuni, har wasu ‘yan kasuwa sun fara zuba hannayen jari.

Musa Alhassan, Malami a Jami’ar Damagaram, ya ce wannan matakji zai bai wa ‘yan kasuwar damar samun wasu karin kudaden shiga a karshen shekara.

“Ko wanne dan kasuwa da ya kawo hannun jari a wannan kamfani da za a sa, ya zama kamar na su, duk matakin da za a dauka wajen kula da Kasuwar Dole da su za a yi, kenan idan aka ci riba a ko wacce shekara ko wanne dan kasuwa zai samu.” Alhassan ya ce.

Saurari rahoton Tamar Abari domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

An Nemi 'Yan kasuwa Da Su Saka Hannun Jari a Kasuwar Dole Ta Damagaram - 2'03