Mataimakin babban lauyan Amurka, Rod Rosenstein, ya ce “Na ‘kayyyade cewa samar da mai bincike na musamman ko mai zaman kansa, ya zama wajibi, domin Amurkawa su samu cikakken kwarin gwiwar sakamakon da zai fito.”
Robert, wanda shine ya shugabanci hukumar binciken laifuka ta FBI daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2013, wanda daga hannunsa ne tsohon shugaban hukumar James Comey wanda Trump ya sallama a makon da ya gabata, ya karbi shugabancin.
Kadan daga cikin ‘yan Majalisu daga jam’iyyar Republican a Majalisa, da kuma ‘yan Democrat, suna ta kira da samar da mai bincike na musamman mai zaman kansa ko wata hukuma don yin binciken alakar da ke tsakanin kwamitin kamfen Trump da ‘kasar Rasha, bincike da zurfinsa ya wuce wanda hukumar FBI ta gudanar da kuma wanda kwamitin Majalisa kan bayanan sirri suka yi a Majalisar Dokoki da Wakilai.
Kiraye-kirayen a nada wannan mai bincike na musamman dai ya yi ‘kamari a ‘yan kwanakin nan, tun bayan sallamar Comey da kuma lokacin da aka fitar da rahotan cewa Comey ya rubuta ganawar da ya yi da Trump, wanda ya bukace shi da ya dakatar da binciken da yake gudanarwa kan tsohon mai baiwa Trump shawara akan harkokin tsaron cikin gida Michael Flynn.