An nada daraktan gudanarwa na hukumar dakile cin hanci da rashawa ta EFCC, Mohammed Umar a matsayin sabon shugaban riko na hukumar.
WASHINGTON D.C. —
A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) wani babban jami'i a hukumar ne ya bayyana hakan.
Hakan duk na faruwa ne bayan da aka dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar ta EFCC.
Kafin nan ya fuskanci wani kwamiti wanda Shugaba Buhari ya kafa domin bincikensa kan wasu zarge-zarge da ake masa.
Da yammacin jiya ma wasu rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da bincike a gidan Magu.
Tun da hukumar ta EFCC ta fito ta musanta labaran da suka ce kama Magu aka yi, bata kara cewa komai ba har yanzu.