An Nada Obasanjo, Kenyatta Su Jagoranci Sulhun Congo

Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) sun nada tsaffin shugabannin Habasha da Kenya da Najeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a jamhuriyar Dimokiradiyyar Congo inda yaki ya kazanta a gabashin kasar.

Da yammacin jiya Litinin, sun fitar da sanarwar cewa sun nada tsohon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a matsayin wadanda za su taimaka wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar sulhu.

A cewar sanarwar manyan manufofin da za su sanya a gaba sun hada da “tsagaita wuta nan take ba tare da gindaya wani sharadi ba” tare da samarda kayan agaji da kuma baiwa filin saukar jiragen saman Goma kariya, daya daga cikin muhimman biranen da kungiyar ‘yan tawayen M23 ta kwace.

Sanarwar ta kara da cewar, a Juma’a mai zuwa kungiyoyin EAC da SADC zasu gudanar da taron ministocin kasashensu “domin tsara jadawalin yarjejeniyar”.

Yayin tarin kolinsu da ya gudana a ranar 8 ga watan Febrairun da muke ciki sun bukaci a tsagaita wuta, saidai an gaza cimma hakan.