An Nada Mai Martaba Aminu Ado Bayero A Matsayin Sabon Sarkin Kano

Sabbin rahotannin sun bayyana cewa ‘yan sa’o’i bayan da gwamnatin jihar Kano ta sauke Muhammadu Sanusi na biyu daga sarautar Kano an nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano.

Mai Martaba Aminu Ado Bayero, dan tsohon sarkin Kano Marigayi Ado Bayero, shine sarkin Bichi kafin wannan nadin.

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, Sanusi Lamido na biyu, tsohon sarkin da aka sauke yana fada ana tantance takardun mika masarautar ga sabon sarki kafin raka shi zuwa jihar da za a tura shi bisa al'ada ya zauna.