'Yan sandan Hadaddiyar Daular Larabawa sun mika sanannen dan Najeriyan nan da ake zargi da damfara, Raymond Igbalode, (inkiya Hushpuppi) zuwa ga hukumar bincike ta FBI da ke Amurka.
An kama Raymond Igbalode ne tare da wasu 'yan Najeriya kan zargin damfara ta Intanet.
Lamarin ya faru ne a Dubai cikin makon da ya gabata yayin wani samame da 'yan Sandan Dubai suka kai.
Hushpuppi ya shahara kan shafin Instagram wajen nuna yawan kudadensa da kuma motocinsa.
A cikin wadanda aka kama tare da shi akwai Olalekan Ponle wanda aka fi sani da Woodberry.
A cikin wata sanarwar da shugaban hukumar bincike ta FBI Christopher Ray ya fitar, ya yaba wa 'yan sandan Dubai da kama Hushpuppi da Woodberry.
Dukanninsu biyu ne dai 'yan sandan na Dubai zasu mika wa FBI.