A Najeriya, Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki da ke, Kaduna ya mayar da wutar lantarki da ya yanke a gidan Shugaban Najeriya a Jamhuriya ta biyu, marigayi Shehu Shagari da ke Sakkwato, kasa da sa'a 24 da yanke wutar.
Gidan tsohon Shugaban kasa a Jamhuriya ta biyu Alhaji Shehu Shagari ya kasance cikin duhu bayan da kamfanin rarraba wutar na KADCO ya yanke wutar ranar Larabar wannan mako.
Lokacin da wakilin Muryar Amurka ya ziyarci gidan da misalin karfe 7:30 na maraicen ranar Alhamis, kwana daya bayan yanke wutar ya tarar an mayar da ita, kuma mazauna gidan sun tabbatar da cewa ma'aikatan wutar ne suka mayar da ita.
Da yake wakilin na mu bai tarar da mai kula da gidan, Ahmad Shehu Shagari ba, ya Kira shi ta waya, inda yayi masa bayanin abin da ya faru da kuma halin da ake ciki, tare da cewa bai san yadda ake biyan wutar gidan ba saboda ba ma taba ganin an kawo bil ba. Haka ma, ya tuntubi Shugaban sashen sadarwa na kamfanin, Abdul’Aziz Abdullahi, inda ya tabbatar da cewa an yanke wutar kuma an mayar da ita, bayan da aka samu tabbacin za a biya kudin. Ya ce gwamnatin tarayya da ta jaha ce ke biyan kudin wutar.
Harwayau, wakilin na mu ya tambayi mai baiwa gwamnan Sakkwato shawara akan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, ko gwamnatin na da masaniya akan wannan lamarin, inda ya ce “ba hurumin gwamnatin jahar Sakkwato ba ne biyar kudin wutar gidan Shagari.”
Masu sharhi akan lamurran yau da kullum irin Farfesa Bello Daudun Bada na ganin wannan a zaman irin wulakanci da mutanen arewa ke fuskanta daga gwamnatin Najeriya a shekarun nan.
Yanzu dai da yake an mayar da wutar bisa ga alkawarin za a biya bashin da ake bi, abin jira a gani shine yadda al'amarin zai kaya anan gaba, za a ci gaba da biyan kudin ko za a bai wa iyalansa dawainiyar biyan kudin ne?
Ga Muhammadu Nasir da cikakken rahoton ta sauti:
Your browser doesn’t support HTML5