An Mance Da Matsalolin Tashin Hankalin Da Jamhuriyar Afika Ta Tsakiya Take Fuskanta 

  • Murtala Sanyinna

CAFRICA-CRIME-ASSUALT-WOMEN

Yara da mata suna cikin rukunin al'ummar da ya fi jin radadin matsalolin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a wannan yankin na Afirka musamman mata wadanda suke cikin barazanar lalata.

Wata bita da kwararru masu zaman kansu na Majalisar Dinkin Duniya suka yi kan halin da ake ciki na kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya nuna yawaitar rikicin kabilanci da kuma cin zarafi mai tsanani a duk fadin kasar, inda yara kanana suka fi fama da munanan cin zarafi a hannun kungiyoyi masu dauke da makamai, da jami’an tsaro, da kuma kamfanonin sojoji da na tsaro masu zaman kansu.

"Abu ne mai wuya a samu wata kasa da ke da tarihin kare hakkin dan Adam mai matukar tayar da hankali, da sauran kasashen duniya suka manta da ita," in ji Volker Türk, babban kwamishinan kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, a jawabin sa na bude taron majalisar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma'a.

Ya ce "Mutanen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suna fuskantar yanayin yau da kullun na tashin hankali ba zato ba tsammani, inda ake amfani da tsoro a matsayin makami da mummunan rauni, wanda tashin hankali na shekaru ya haifar."

Ya ce yara ba su tsira daga barnar da rikicin da ya barke tun a shekarar 2012 ya haifar ba, inda ya ce musamman ‘yan mata na fuskantar munanan ayyukan lalata da ke da alaka da rikicin.