A wani jawabi da ya yi kai tsaye ta gidan talabijin din kasar, shugaba Lazarus ya ce cire janar Vincent Nundwe da aka yi baya bisa tsari.
Ya ce “duk da yake tsohon shugaban kasa hakkin dakarun kasar Malawi ya na wuyansa, a matsayinsa da shugaban sojoji, kuma yana da ikon nada duk wanda yake so a kowanne mukami, abu ne maras kyau ayi amfani da irin wannan iko ba tare da dalili ba. saboda haka, na dawo da Janar Nundwe a matsayin shugaban dakarun Malawi.”
Tsohon shugaban kasar Malawi, Peter Mutharika, shine ya kori Nundwe a watan Maris saboda ya bar sojoji sun kare masu zanga-zangar kin amincewa da zaben shekarar da ta gabata.
Daga bisani, kotun tsarin Mulki ta yi watsi da zaben ta kuma nemi a sake sabon zabe, wanda Chakwera ya lashe a watan Yunin wannan shekarar.
Chakera ya ce shawarar da ya yanke ta sake dawowa da Nundwe ya yi ta ne domin dawo da adalci ga ayyukan dakarun tsaron kasar.