An Kwakulewa Wata ‘Yar Gudun Hijira Idanunta A Jihar Adamawa

Yaganama 'yar gudun hijira da aka jire idanunta a Yola, jihar Adamawa

Wasu muggan mutane sun sace wata ‘yar gudun hijira mai suna Yaganama suka kwakule idanunta biyu kafin su jefar da ita kan hanya inda aka tsinceta aka ji mata jinya duk da dai ta rasa idanunta

Wasu da ba’a tantance ba sun sace ‘yar gudun hijira Yaganama dake da tabin hankali wadda ta fice daga sansanin ‘yan gudun hijira na Makohi suka kaita wani waje inda suka kwakule idanunta daga bisani kuma suka jefar da ita akan hanyar Fufure. A nan aka tsiceta aka kaita asibiti a Yola.

Yaganama ta fito ne daga karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno inda rikicin Boko Haram y araba mutane da gidajensu.

Wannan’yar talika dai tana cikin wani mawuyacin hali ne saboda bata da idanu bata kuma iya magana sai dai yarenta. Wata Malama Maggdaline Bitrus na cikin wadanda suke kula da ita a sansanin. Ta ce basu san yadda zasu yi da it aba saboda futsari da bayan gida sai dai a kaita ta yi. Tana bukatar a yi mata jinya kana a nemi ‘yanuwanta da zasu ci gaba da kula da ita.

Malama Fatima Umar shugaban matan sansanin, ta ce lamarin ya tada masu hankali ainun. Injita akwai da yawa dake dake da tabin hankali a cikinsu. A daukesu a kaisu inda za’a yi masu magani kana a nemi ‘yanuwansu.

Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA dake kula da sansanonin ‘yan gudun hijira ta tofa albarkacin bakinta akan abun takaicin da ya auku. Imam Abani Garki jami’in hukumar mai kula da jihohin Adamawa da Taraba ya godewa asibitin gwamnatin tarayya dake Yola da hukumomin jiha da wata kungiyar kasa da kasa saboda taimakon da aka ba Yaganama wadda y ace yanzu ta samu lafiya kuma tana zaune cikin ‘yanuwa.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Bacewa Jirgin Gwamnatin Nijar Ya Yi? – 2’ 48”