A shekaru masu zuwa za a ga kananan jirage da zasu dauki mutane kamar yanda motocin tasi ke yi, wanda zasu iya tafiya mai nisa cikin dan karamin lokaci ba kamar yanda motocin tasi suka saba ba, a cewa jami'ar Michigan.
Kamfanoni da dama suna aiki gadan-gadan domin kera kananan jirage da ake kira VOLT da zasu dauki fasinjoji, su yi tafiyar kilomita 160 a cikin sa’a guda kuma su sauka a kan kananan filaye a cikin birane masu cike da jama’a.
Masu bincike sun ce irin wadannan ababen hawa zasu kawo saukin gurbatar yanayi da ake samu ta hayakin ababen hawa da mutane uku ke shaka a kowane tafiya da zasu yi na kilomita 100. Sai dai za a samu hakan ne idan fasinjoji sun amince da amfani da irin wannan abin hawa fiye da mota.
Wannan karamin jirgin (VOLT) zai fi samun kasuwa musamman game da makamashin da zai yi amfani da shi da kuma rashin gurabata yanayi, inji Gregory Keoleian na jami’ar Michgan a cikin wata sanarwa.
Jiragen VOLT zasu dauki fasinja fiye da motoci a wurin tafiyan misali, daga San Francisco zuwa San Jose ko kuma daga Detroit zuwa Cleveland.
Masana dake aiki da masu bincike a kamfanin kera motoci na Ford, sun gano cewa VOLT na bukatar makamashi mai yawa da zai iya tashi sama, amma kuma zasu yi aiki fiye da motoci.