Wani Alkali a Hawaii ya takawa umarni na biyu birki da ya bukaci a dakatar da tsarin ba ‘yan gudun hijira mafaka, da kuma dakatar da ba da takardun izinin shiga Amurka-VISA- ga mutane daga wadansu kasashe shida.
Wani alkalin gwamnatin tarayya a jihar Maryland shi ma ya ambaci kalaman Trump yayin da ya ke ba da umarnin watsi da dokar yau alhamis, sai dai hukuncin ya shafi umarnin hana ba da takardar visa ne kawai na dokar da shugaban kasar ya zartas, ba tsarin ba ‘yan gudun hijira mafaka ba.
Alkali Derrick Watson ya bayyana a jiya Laraba cewa, yana yiwu wa hujjar da jihar Hawaii ta bayar cewa, dokar ta sabawa kundin tsarin mulkin kasa da ya bukaci gwamnati ta cire batun addini a dukan matakan da za ta dauka, ta sami karbuwa.
Ya ambaci kalaman da Trump da mukarrabansa suka rika yi kafin zaben da kuma bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.
A lokacin da yake yakin neman zabe, Shugaba Trump ya yi kira da a hana dukan Musulmi shiga Amurka, abin da aka sauya daga baya aka bukaci sa ido sosai kan mutanen da suka fito daga kasashen da ake alakantawa da ayyukan ta’addanci.