An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Sudan

Masu zanga zanga a birnin Khartoum na Sudan, Yuli 18, 2019.

Ana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da aiki, kan yadda za a shata jadawalin wannan gamayya.

Mai shiga tsakani a rikicin siyasar Sudan na kungiyar tarayyar Afirka, ya ce Majalisar Mulkin Sojin kasar da shugabannin masu zanga zanga, sun cimma wata matsaya ta kafa gwamntin wucin gadi da za ta kwashe shekaru uku tana mulki, kafin a yi zaben da zai samar da mulkin farar hula.

Mai sulhu Mohammad Hassan Lebatt, wanda Kungiyar tarayyar Afirka ta nada, ya sanar da wannan matsaya, ba tare da ya fadada bayanansa ba.

“Ina mai sanar da al’umar Sudan da Afirka da kuma kasashen duniya cewa, wakilan bangarorin biyu, sun amince da wannan yarjejeniya.” In ji Lebatt.

Ana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da aiki, kan yadda za a shata jadawalin wannan gamayya.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, ya ruwaito cewa a gobe Lahadi ake sa ran bangarorin sojin da na shugabannin masu zanga zangar za su rattaba hannu kan wannan yarjejeniya.

Sudan dai ta kwashe watanni tana fama da rikicin siyasa inda aka yi ta zanga zanga, wacce ta faro tun daga watan Disambar bara, sanadiyar tsadar man fetur, lamarin da ya kai ga sojin kasar suka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Al Bashir a ranar 11 ga watan Afrilun bana, wanda ya kwashe shekaru 30 yana shugabantar kasar.