An Kulla Yarjejeniyar Kafa Gwamnatin Hadaka a Sudan

Wakilan bangarorin dakarun Sudan da na shugabannin masu zanga zanga a lokacin da aka kulla yarjejeniyar kafa gwamantin hadaka

Gabanin a kai ga cimma wannan matsaya, an kwashe watanni ana jerin zanga zanga, wadanda suka faro tun daga watan Disambar bara, kan tsadar farashin man fetur.

Majalisar Mulkin Soji da shugabannin masu zanga zanga a Sudan, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da tarihi, wacce za ta ba da damar rarraba mukamai a gwamnatin wucin gadin da za a kafa a Khartoum, babban birnin kasar.

Wannan matsaya da aka cimma, ta samar da gwaamnatin hadakar da ta hada da sojojin kasar da kuma fararen hula, wacce za ta tafiyar da ragamar mulkin kasar har na tsawon shekara uku, kafin a yi zaben da zai mika mulki ga farar hula.

Gabanin a kai ga cimma wannan matsaya, an kwashe watanni ana jerin zanga zanga, wadanda suka faro tun daga watan Disambar bara, kan tsadar farashin man fetur.

Daga bisani zanga zangar ta jirkice ta koma ta neman tsohon shugaban kasar, Omar Al Bashir ya sauka daga mukaminsa.

Hakan ya sa dakarun kasar suka hambarar da gwamnatinsa watan Afrilu, amma duk da hakan, masu zanga zanga ba su janye boren da suke yi ba, inda suka rika kiran a yi sauye-sauye a fannin mulkin dimokradiyya kasar, bayan shekaru 30 da Al Bashir ya yi yana mulkarsu.