Jam'iyya mai mulkin kasar Liberia ta ce ta kori shugabar kasar mai barin gado,Ellen Johnson Sirleaf, domin ta ki ta marawa mataimakin shugaban kasar baya a zaben da aka kammala kwanan nan.
WASHINGTON D.C. —
Jam'iyya mai mulki a kasar Liberia ta sallami shugabar kasar Liberia mai shirin ajiye mulki kwanan nan, Ellen Johnson Sirleaf daga jamiyyar.
Jam'iyyar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin ta ki ta mara wa mataimakin shugaban kasa baya, Joseph Boakai, wanda ya tsaya takarar shugaba kasa karkashin jam'iyyar a zaben da aka kammala kwanan nan.
Boakai dai shi ne ya yi mataimakin shugaban kasa karkashin jagorancin shugaba Sirleaf har na tsawon shekaru 12.
Amma ya fadi zabe wanda tsohon dan wasan kwallon kafa George Weah ya yi nasara.
Sirleaf wadda ta kwashe wa'adin mulki biyu, ba ta damar sake tsayawa takara kamar yadda dokar kasar ta Liberia ya tanada.