An Kori Boko Haram Daga Garin Kerawa Na Janhuriyar Kamaru

  • Ibrahim Garba

Shugaba Paul Biya na Kamaru

Da alamar dai haka ta fara cim ma ruwa, game da shiga sojojin Amurka kasar Kamaru don taimakawa wajen yakar Boko Haram saboda a yanzu ta tabbata cewa an fatattaki 'yan Boko Haram daga garin Kerawa na Kamaru.

A wani al’amari mai kama da hobbasar sojojin Amurka ta farko a kasar Kamaru, sun tabuka a wata fatattakar da sojojin gamayyar Afirka su ka yi ma Boko Haram a Janhuriyar Kamaru.

Wakilin Sashin Hausa Muhammed Garba Awwal ya ce an fafari Boko Haram daga garin Kerawa, wanda su ka abka masa a karshen mako, su ka kashe jama’a tare da wawurar dukiyoyinsu, su ka kafa tutocinsu kafin wannan samamen da aka kai masu .

Wakilin Hausa y ace bayan wannan nasarar da sojoji su ka yi, manema labarai da Magajin Garin karamar Hukumar Mayo-Sava da sauran jami’an gwamnati sun isa garin inda su ka yi ta kokarin kwantar ma jama’a hankula.

Kwamandan da ya jagoranci wannan samamen Babila-Akau ya bayyana ma manema labarai yadda su ka fatattaki ‘yan Boko Haram tare da cire tutocinsu da cewa yanzu an kori ‘yan ta’addar daga arewacin Kamaru don haka jama’a su kwantar da hankulansu. Su ma ‘yan garin na Kerawa sun bayyaba jin dadinsu da korar Boko Haram da aka yi daga garin.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kori Boko Haram Daga Kerawa, Kamaru - 6' 12''