An Koka Kan Rashin Mata Musulmai A Faggen Wasan Kwallon Kafa

Kwallon mata

Ganin yadda kasashen duniya ke son maida kwallon kafar mata ya zama wani sana’a, a wannan karni damuke ciki amma mata Musulmai, na kasashen nahiyar Afirka, ta yamma tama nahiyar Afirka, ta tsakiya ba kasafai suke daukar wannan sana’a wani abin a zo a gani ba.

Wannan alamari dai yana daurewa wadansu mazauna kasar Kamaru, kai a yayin da mata nahiyar Afirka, suke taka leda na cin kofin kwallon kafa na mata a nahiyar Afirka, a kasar Kamaru.

Najeriya, zata kara da kasar Kamaru a wasan karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na mata ranar asabar.

Malam Zakari ma’abucin wasan kwallon kafa ne ya nuna rashin jindadinsa na yadda mata Musulmai basu shiga cikin takwarorinsu mata domin cirewa kansu kitse a wuta maimakon wani sana’a wanda baiya kaisu ga tudun na tsira.

Your browser doesn’t support HTML5

An Koka Kan Rashin Mata Musulmai A Faggen Wasan Kwallon Kafa - 2'03"